A wata sanarwa da Shugaban jam’iyyar APC ta rivers Dr. Davies Ibiamu Ikanya ya fidda tace: ”Mutane sun hadu daban daban sun taye Amaechi murna akan nasarorin daya samu. Kuma sunyi Allah wadai da binciken ganin kwab da Nyesom Wike yake kokarin yima Amaechi.”
Suka ce: “Haramtaccen zaman da yakeyi a gidan gwamnati a Port Hacourt har na tsawan wata 2 ya kusa zuwa karshe. Kuma sunyi Allah wadai da binciken ganin kwab da Nyesom Wike yake kokarin yima Amaechi.”
Yace: “Abunda wike yake kokarin yi kamar misalin mutum ya ciji hannun dake bashi abinci ne. Mu baza mu damu ba don shi yana kokari ya tozarta mutumin kirki ne. Kuma shi Wike gwamnan wucin gadi ne.
“Muna mika godiya ta musamman ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, maitaimakin shi Farfesa Osinbajo, Gwamnar El rufai, gwamnan Jos, Uwar gidan shugaban kasa A’isha Buhari da kuma Shugaban jam’iyyar APC ta kasa Oyegun.”
Jam’iyyar kuma ta ba Wike shawara yabi a hankali akan yadda yake gudanar da abubuwan shi.
DSB has launched its Hausa service.
Please help us to improve our quality by rating the clarity of language
in the article above
Tags
Politics
